HIJABI akan mace musulma

Allah Madaukakin Sarki yace "Ya kai wannan Annabi, Fadawa Matanka da 'Ya'yanka Mata, da kuma Matan Muminai (cewa), Su yafa Mayafansu. Wannanan Shi yafi kusanci da A gane Su. Don kada A cucesu. Allah kuma ya kasance mai gafara ne Mai rahama" 
 (Suratul Ahzab 59).

Saboda haka kada ko wace mata ta ajiye hijabi, wai Don wasu
na amfani da hijabi suyi ta'addanci. Babu shakka masu
neman bata sunan Islam ne, haka kuma Allah yayi alkawarin
daukaka addininsa ko kafirai sunki.
Shugaban yace Hatsari ne babba ga alummar da suka bar
iyalansu na fita babu hijabi. Allah Shine Wadda yayi ummurni
da sallah da Azumi da zakka da hajji shi ne kuma yayi umurni
da sanya hijabi. Saboda haka mata musulmai ku lizimci hijabi
da istigfari, Domin hakan zai sa Mahaliccinmu ya tausaya
mana.
Allah ya azurta mu dayi masa da'a da bindokokin sa. Allah ya
bamu zaman lafiya Mai dorewa a kasa. Amin.Kabiyomu domin saurar fadakarwa:
Facebook  like   Twitter follow Istagram follow


Post a Comment

0 Comments