TAMBAYA: Mace idan ta xauki wani lokaci ba ta ga al’adarta ba, alhalin bata da miji ya za ta yi?

TAMBAYA: Mace idan ta xauki wani lokaci ba ta ga
al’adarta ba, alhalin bata da miji ya za ta yi?
AMSA: Mai yiwuwa ta tava yin ala’dar ne ta xauke ko kuwa
ba ta tava yi ba, ba ta fara ba.
Idan ba ta fara ba kwata-kwata, to lokacin zuwanta ne
bai yi ba.
Malamai sun ce mafi qarancin shekarun da amce take
fara ala’da shi ne shekara tara (9) kuma mafi
tsawonlokaci shi ne shekara 50. Don haka idan mace kafin
shekara tara (9) taga wani jinni ya fito mata ko bayan
shekara 50 ta ga jinni ya fito mata to wannan jinin na
rshin lafiya ne.
Amma daga shekara 9 har zuwa wani lokaci mai tsawo
kamar shekara 15 idan duk ba ta ga ala’darta ba, ba wani
abu ba ne lokacinsa ne bai yi ba ko bai fito ba, idan kuma
ta fara sai kwata-kwata ya xauke ya dena zuwa to, dama
malamai sun kasa mata kasha uku:
i. Akwai mai yin ala’da wata-wata
ii. Akwai mai yin ala’da bayan lokaci-lokaci, Kamar wata
uku-uku ko shida-shida ko kuma shekara-shekara
iii. Akwai kuma wacce gaba xaya ba ta yin ala’dar ma.
Idan tana ganin wata lalura c eta sa al’adar ta xauke wa
kuma ba wani magani ta shada zai sanya al’adarta xauke
ba, to sai a nemi likita domin samun bayani.

Post a Comment

0 Comments