TAMBAYA: Akwai salloli ne da ba a kamar su har sai rana ta fai kamar Sallar Asubah da Sallar La’asar, Menene qarin bayani?

TAMBAYA: Akwai salloli ne da ba a kamar su har sai
rana ta fai kamar Sallar Asubah da Sallar La’asar,
Menene qarin bayani?
AMSA: Ita sallah tana tserewa mutum da dalilai guda uku:
1. Mantuwa 2. Bacci 3. Ganganci.
Wanda Sallah ta tserewa saboda dalili na mantuwa ko
bacci, manzon Allah 9S.A.W) ya ce, “Wanda ya yi bacci ga
barin sallah ko ya manta, to ya slala c eta lokacin da ya
tuna ta ko da daddare ko da rana, ko kuma kowane
lokaci.
Lokacin da ya tuna ta ko da sallar da rana ake yinta sai
ya tuna da daddare to ba zai bari sai rana ta fito ya
rama ta ba.
Aka ana binsa sallar da ake yi da rana bai tuna ba sai da
daddare kamar azahar da la’asar, to da daddaren zai yi
ta. Hakanan sallolin da ake bisna bashikamar asuba da
magariba da isha, sai ya tuna su da tsakar rana, to
lokacin da ya tuna su shi ne lokacin su.
Wanda ya bar sallah da gangan, wannan hatsarinsa yana
da girma.
Wannan aya ta figitar da mu cewa lallai bay a halatta
Musulmi ya bar salla da gangan. Idan ya bari kuwa
malamai sun yi maganganu guda biyu:
i. Wasu Malamai sun ce ta shekara goma (10) sai ya rama
ta sannan ya nemi Allah 9S.W.T) ya yafe mas.a
ii. Wasu Malamai sun ce sai dai ya yi ta kuka yana tuba da
nadama ya kuma cika sharaxan tuba guda 5. Da suka haxa
da tuba saboda Allah, da nadama da qoqari ya yi akan
lokaci yanzu da alqawarin ba zai sake yi ba da kuma ya
zamo tuban ya yi shi ne kafin rana ta hudo ta yamma, ba
kuma dai-dai lokacin da zai mutu ba, in kuma a dai-dai
lokacin da zai mutu ne to Allah ba zai karvi wannan tuban
ba.
Saboda haka ko wane lokaci aka tuna sallah ana yinta ko
da rana ko da kuwa sallar ta dare ce ko da dare ko da
sallar ta rana ce.

Post a Comment

0 Comments